1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Rawar Afirka ta Kudu a siyasar duniya

Martina Schwikowski LMJ/SB
May 28, 2024

Kasar Afirka ta Kudu, ita ce mafi karfin tattalin arzikin masana'antu a tsakanin takwarorinta na nahiyar Afirka. Kasancewarta mamba a kungiyar Kasashen da Tattalin Arzikinsu ke Habaka Cikin Hanzari ta BRICS.

https://p.dw.com/p/4gNo1
Shirye-shiryen zaben Afirka ta Kudu | 2024
Shirye-shiryen zaben Afirka ta KuduHoto: Themba Hadebe/AP Photo/picture alliance

Afirka ta Kudu dai ta kasance ja gaba wajen tabbatar da wanzuwar zaman lafiya da sulhunta rikici a kasashen nahiyar Afirka, misali rikicin kasar Habasha da yankin Tigray a shekara ta 2022. Sai dai ba a Afirka kawai ta tsaya ba har ma a duniya baki daya, domin kuwa Shugaba Cyril Ramaphosa na Afirka ta Kudun, ya yi kokarin sasanta rikicin Rasha da Ukraine. A watan Yunin 2023, Shugaba Ramaphosa ya tattauna ta wayar tarho da shugaban kasar Rasha Vladmir Putin da takwaransa na Ukraine Volodymyr Zelensky tare da jagorantar wata tawaga ta shugabannin kasashen Afirkan zuwa Moscow da kuma Kiev.

Karin Bayani: Zaben Afirka ta Kudu ya soma

Afirka ta Kudu da sauran kasashen BRICS
Afirka ta Kudu da sauran kasashen BRICSHoto: Prime Ministers Office/Zuma Press/picture alliance

Afirka ta Kudu ta ci gaba da zama a tsaka-tsaki, koda yake tun bayan yakin cacar-baka kasar tare da Rasha suke dasawa da juna. Wannan dangantaka ta sanya Kasashen Yamma da dama, yin rowar kuri'unsu a babban zauren Majalisar Dinkin Duniya. Bayan barkewar yaki tsakanin sojojin Isra'ila da kungiyar Hamas da ke gwagwarmaya da makamai a yankin Zirin Gaza na Falasdinu, Afirka ta Kudu ta maka mahukuntan Tel Aviv a babbar kotun Majalisar Dinkin Duniya da ke birnin The Heague na kasar Neatherlands kan abin da ta kira kisan kare-dangi da take zarginsu da aikatawa a Gaza.

A ranar 24 ga wannan watan na Mayu, kotun ta bayar da umurnin dakatar da hare-haren Isra'ila a yankin Rafah na Zirin Gazan nan take kamar yadda Afirka ta Kudun ta nema a yi cikin gaggawa. Sai dai gwamnatin Pretoria na yawan shan suka kan daukar wannan mataki dangane da Falasdinawa, amma ta yi mirsisi kan wasu dokokin kasa da kasa da Rasha ke takewa a Ukraine. Duk da sukan da Afirka ta Kudu ke sha daga Kasashen Yamma musamman ma Amurka, kasar na son samar da ra'ayi kan goyon bayan Falasdinawa ba wanda yake nuna karfa-karfa ba sai dai wanda kofarsa take a bude domin tattaunawa.

Shirye-shiryen zaben Afirka ta Kudu
Shirye-shiryen zaben Afirka ta KuduHoto: MARCO LONGARI/AFP

Ba kamar wanda ya gada Jocob Zuma ba, Shugaba Cyril Ramaphosa na Afirka ta Kudu na kokarin karfafa dangantakar kasa da kasa da a baya kasar ke da ita tun farkon mulkin dimukuradiyya. Bayan kwashe tsawon lokaci a matsayin saniyar ware da kuma mulkin wariyar launin fata, Afirka ta Kudu karkashin shugabancin marigayi Nelson Mandela ta yi kokarin inganta hulda da kasashen ketare domin ta koma cikin dangi.

Wannan a bayyane yake a rawar da take takawa a kungiyar Tarayyar Afirka da kuma kasancewarta kungiya daya tilo ta Afirka da ke cikin kungiyar Kasashe masu Karfin Tattalin Arziki a Duniya ta G20, baya ga kasancewarta mamba a kungiyar BRICS ta Kasashen da Tattalin Arzikinsu ke Bunkasa Cikin Hanzari da a yanzu ke da mambobi tara domin samun karfin fada a ji a Majalisar Dinkin Duniya da Asusun ba da Lamuni na Duniya da ma kungiyar Kasuwanci ta Duniya. A farkon wannan shekara ta 2024, kungiyar BRICS ta samar da bankinta na kanta kuma Afirka ta Kudu na taka muhimmiyar rawa wajen samar da bangaren tattalin arziki da zai yi kan-kan-kan da na kasashen da suka ci-gaba.