1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Isra'ila ta ragargaza cibiyar sojoji a Siriya

December 10, 2024

A cikin sa'o'i 48 da suka gabata, kimanin luguden wuta 250 ne Isra'ilan ta yi wa Siriya domin lalata karfin soji da rumbunan makaman kasar Siriya, a cewar kungiyar Syrian Observatory for Human Rights.

https://p.dw.com/p/4nweT
Hoto: Kobi Gideon/Israel Gpo via ZUMA Press Wire/picture alliance

Dakarun Isra'ila sun ragargaza cibiyar sojoji mafi muhimmanci ta kasar Siriya. Hakan ya faru ne a yayin wasu sabbin hare-hare da Isra'ila ta kaddamar tun bayan faduwar gwamnatin Bashar al-Assad.

Ministan harkokin wajen Isra'ila Gideon Saar ya ce wadannan hare-hare da kasarsa ta kaddamar kusa da iyakarta da Siriya a tuddan Golan inda Isra'ilan ta mamaye, ta yi haka ne domin inganta tsarontana cikin gida, kuma a cewarsa matakai ne na wucin gadi ba na din-din ba.

Har kawo safiyar wannan Talata dai kamfanin dillancin labarai na Faransa, AFP, ya ce ana ci gaba da jin karar abubuwa masu fashewa a birnin Damascus, hedikwatar mulkin kasar Siriya.