1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dambarwar siyasa a kasar Kenya

Abdullahi Tanko Bala
November 2, 2017

Wata kungiya ta masu fafutukar kare hakkin bil'adama a Kenya ta zargi 'yan sandan kasar da kisan masu zanga-zang biyo bayan zagaye na biyu na zaben shugaban kasar.

https://p.dw.com/p/2mwS5
Kenia Wahlen - Ausschreitungen in Nairobi
Hoto: Reuters/G. Tomasevic

Kungiyar ta ce 'yan sanda sun yi anfani da karfin da ya wuce kima a rikicin da ya barke a yayin sake zaben shugaban kasar, baya ga haka ta ce ta tattara bayanai ta hanyar anfani da kimiyar zamani don bai wa iyalai ko wadanda lamarin ya shafa sheda don shigar da kara kan cin zarafin da suka fuskanta da ma wadanda suka rasa wani nasu.

A watan da ya gabata kungiyar Amnesty International da Human Rights Watch da ke rajin kare hakkin dan Adam sun ce 'yan sanda a Kenya sun halaka magoya bayan jam'iyyar adawa 67 a rikicin da ya barke bayan da kotun koli ta soke sakamakon zaben farko da ya gudana a watan Agusta.