Harin Magdeburg zai zama maudi'i a yakin neman zaben Jamus?
December 23, 2024Kasa da sa'a guda bayan harin da aka kai a kasuwar Kirsimeti ta garin Magdeburg da ke Jamus aka fara samun 'yan siyasa da ake gani suna amfani na lamarin wajen karfafa matsayinsu a siyasance tare da yada bayanai marasa tushe bare makama. 'Yan siyasa irin Martin Sellner mai matsanancin ra'ayi na kasar Austria yana kan gaba a nahiyar Turai cikin 'yan siyasa wajen yada bayanai marasa inganci.
Karin bayani: Jamus na tuni da harin kasuwan Krismeti
Sven Tritschler mataimakin bangaren 'yan majalisa na jam'iyyar AfD mai kyamar baki a majalisar dokokin jihar North Rhine-Westphalia wadda take zama jiha mafi yawan mutane a Jamus, ya ce tuntuni jam'iyyarsu ta sallami mutumin da ya kai wannan hari. Shi kuwa Benjamin Höhne da ke zama masanin harkokin siyasa kana mai bincike kan jam'iyyu na ganin haka a matsayin lamarin siyasa da zai kara takura batun samun mafaka ga bakin haure.
Höhne ya ce: "Haka abin yake tafiya, ana kara komawa zuwa matsanancin ra'ayi. Bude kofa ga manufofin baki saboda kare hakkin dan Adam abu ne da ya ja-baya. Kuma irin wannan hari na Magdeburg na matse yanayin."
Ita dai jam'iyyar AfD mai kyamar baki tana gani yanayin da milyoyin mutane suke kokarin tserewa daga inda suke rayuwa ne ke kawo matsalolin tsaro a Jamus, kuma sake mayar da milyoyin mutanen inda suka fito shi ne mafita. Ita kanta shugabar jam'iyyar AfD ta kasa kuma 'yar takarar mukamun shugabar gwamnati, Alice Weidel bayan harin da aka kai a Jamus, ta yi wani shagube a shafinta na sada zumunta tana mai cewa "Yaushe wannan wautar za ta kawo karshe" kuma wannan na zuwa jim kadan gabanin zaben kasa baki daya da zai gudana a watan Fabreru na shekarar 2025.
Karin bayani: Yinkurin kai hari a Jamus ya ci tura
'Yan siyasa da dama sun soki Nancy Faeser da ke zama ministar harkokin cikin gida na Jamus saboda gazawa wajen daukan matakan da suka dace, duk da cewa hukumomin Saudiyya sun gargadi mahukuntan Jamus kan wannan mahari. Saboda haka ne Benjamin Höhne, masanin harkokin siyasa kana mai bincike kan jam'iyyu ke ganin cewar 'yan siyasa musamman masu matsanancin ra'ayi za su daura alhakin haka kan gwamnatin tarrayar Jamus
Benjamis Höhne ya ce: "Ana iya tunanin cewa duk jam'iyyun siyasa, musamman masu matsanancin ra'ayi, za su nuna tsangwama ga ministar cikin gida da jam'iyyar SPD game da yanayin da ake ciki na tsaro. Saboda jam'iyyar SPD ita ce ke da alhakin kula da ma'aikatar cikin gida gami da tsaron kasa a matakin tarayya, sannan ita kuma za ta yi kokarin kare kanta saboda manufofi a bangaren Magdeburg."
Karin bayani: Jamus: Yiwuwar samun farmakin kyama
Har daga kasashen ketare, akwai masu katsalandan kan zaben Jamus, inda hamshakin mai arziki na Amurka, Elon Musk ya shiga cikin wadanda suka caccaki gwamnatin Jamus bayan harin na garin Magdeburg, har ya bukaci shugaban gwamnati Olaf Scholz da ya ajiye aiki.