Bikin Kirsimeti: Ranar bayar da kyaututtuka
December 26, 2024Mabiya Addinin Kiristan a Najeriyar dai, na rararraba kyaututtukan da suka hadar da kayan abinci da sauran kayan kwalam da makulashe ga abokan zamansu mabiya sauran addinai a ranar 26 ga watan Disamaba da ta kasance ta bayar da kyaututtuka wato Boxing Day bayan Bikin Kirsimeti da ake a ranakun 25 ga watan na Disambar kowacce shekara. Pastor Dakta Yohanna Y D Buru ne dai ya jagoranc mabiyansa, wajen rarraba kyaututtuka ga makwabta da mabukata da zummar kara kulla kyakkyawar danganta da zamantakewa a tsakanin dukkanin al'umma ba tare da lura da irin yanayin addininsa ko banbamcin kabila ba. Baya ga kayayyakin abinci da sutura da ake rarrabawa, akwai akwatunan da ke kunshe da wasu kayayyaki da ake bai wa makwabtan.
Mallam Gambo Abdullahi Barnawa na daga cikin wadanda suka samu kyautar a karan farko, inda kuma ya tabbatar da cewa wannan wani yunkuri ne na kara samun hadin kan alummar kasa da samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali. Wadannan kyaututtuka dai na zuwa ne, a daidai lokacin da al'ummar Najeriyar ke fama da matsalar tsadar rayuwa da ta tsaro tare da hauhawar farashin kayayyakin abinci. Jihar Kaduna dai ta yi nasarar samun zaman lafiya a wannan shekarar ta 2024 da ke karewa, inda rahotannin da Hukumar Samar da Zaman Lafiya ta fiatar suka nunar da cewa babu wani tashin hankali da aka samu da ke da nasaba da kabilanci ko addinai da rigimar masarautun gargajiya. Wanna dai ya sanya gwamnatin jihar, yin jinjina ga al'ummarta a kan jajircewa wajen rungumar zaman lafiya maimakon tashin hankali.