Senegal za ta soma fitar da iskar gas daga badi
October 18, 2022Senegal ta sanar da gano albarkatun mai da iskar gas, wadanda take fatan dogaro a kansu wajen bunkasa tattalin arzikinta tare da habbaka masana'antun kasar. Amma a birnin Saint-Louis da ke arewacin kasar inda ake da tashar iskar gas a bakin teku, masunta sun koka kan asarar arzikin kifi da wannan yankin ke tafkawa.
Wannan tashar iskar gas ta kasance a cikin tekun Atlantika a kimanin kilomita goma da gabar ruwan birnin Saint-Louis, da ke kan iyaka tsakanin Senegal da kasar Mauritaniya. Sai dai bututayen jigilar iskar gas da aka dasa a garin bai yi wa Moussa Fall wani mai sana'ar kamun kifi dadi ba, saboda yadda rayuwarsa ta yi rauni sakamakon karancin kudin shiga.
Gwamnatin ta Senegal ta shirya fara fitar da iskar gas a shekara ta 2023. Sai dai a yayin da wannan wa'adi ke dada gabatowa, hukumomin kasar sun kara daukan matakan sa ido a kan dandamalin. A yanzu haka, an kafa shingen bincike tare da aiwatar da sintirin jirgin ruwa don kalubalantar duk wani wanda ke son ketare wani shingen da aka gindaya. Sai dai babban sakatare Janar na kungiyar masunta ta Senegal Moustapha Dieng na cewa, tashar iskar gas din ba za ta iya tafiya kafada da kafada da kamun kifi ba, saboda haka da sake.
A Senegal, arzikin man fetur da iskar gas da kasar ta mallaka ba su fi kashi 0.07% da 0.5% na wadannan arzikin tekun na duniya ba. Amma ga hukumomin birnin Dakar, suna da mahimmanci a ma'auni na kasa kuma dogaro da za a iya kansu wajen samun ci gaban tattalin arziki zai inganta yanayin rayuwar jama'a, musamman samun wutar lantarki. Sai dai wannan hujjar ta kasa samun karbuwa a tsakanin masu gwagwarmaya irin su Pape Fara Diallo, shugaban gamayyar da ake kira "Publiez ce que ous Payez". ma'ana ku bayyana a bin da kuka biya
Baya ga mummunan tasirin a fannin zamantakewar al'umma, masu fafutukar kare muhalli suna fargabar cewa, yin amfani da wadannan albarkatu masu gurbata muhalli za su haifar da illa da ba muhalli bai za a iya jurewa ba, a daidai lokacin da aka tabbatar da cewa burin daidaita dumamar yanayi na duniya a digiri 1.5 ° C, ba za a iya mutunta shi ba.