1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin gudanar da zaben gama gari a Angola

Abdourahamane Hassane RGB
August 23, 2022

Masu lura da al'amura na hasashen cewar za a yi fafatawa mai zafi a tsakanin shugaba Joao Lourenco da madugun adawa Adalberto Costa Junior a zaben kasar Angola.

https://p.dw.com/p/4FvuT
Angola I Wahlen
Hoto: D. Vasconcelos/DW

Jam'iyyun siyasa guda takwas ne za su kara a zaben kasar Angola, sai dai ana ganin fafatawar za ta fi yin zafi a tsakanin jam'iyya mai mulki ta MPLA (Popular Movement for the Liberation of Angola) wacce ke kan karagar mulki tun lokacin samun 'yanci kai a shekarar 1975 da kuma jam'iyyar adawa ta UNITA (The National Union For The Total Independance of Angola) Mutane miliyan 14 da suka cancanci kada kuri'a za su raba gardama a kan kujeru 220 da ake da su a majalisar dokokin Angolan.

Joao Lourenço shugaban kasa mai ci na jam'iyyar MPLA wanda shi ne karo na biyu da yake tsayawa takara, zai fuskanci goggaya mafi karfi daga dan takarar jam'iyyar adawa ta UNITA Adalberto Costa Junior. Masanin siyasar kasar Angola Alex Vines, wanda ke jagorantar sashen Afirka a cibiyar bincike ta Birtaniya ta Chatham House ya ce, akwai zumudi na neman sauyi ga jama'ar kasar.

"Angola kasa ce matashiya kuma matasan Angola suna son a samu sauyi, don haka ne dan takarar jam'iyyar adawa mafi girma ta UNITA ke da farin jini sosai, musamman a manyan biranen Angola biyar, inda mafi yawan 'yan kasar ke zaune." 

Angola I Wahlen
Madugun adawa Adalberto Costa JúniorHoto: D. Vasconcelos/DW

Duk da yadda ake kalon UNITA a matsayin jam'iyyar da ka iya yin bazata a zaben na Angola, Lourenco ya kawo sauye-sauye tare da sabbin ka'idoji wajen samun mallakar kamfanonin a wani martani na goge irin kaurin sunar da kasar ta yi, na cin hanci da karbar rashawa da yin sama da fadi da dukiyar kasar, wanda kusan dangin na tsohon Shugaba Jose Edouardo dos Santos suka rika cin karensu ba babbaka. Wadanda daga bisanni shari'a ta rika tuhumarsu har ma da manyan sojojin kasar. 

Angola - Historischer Diamant gefunden, 170 Karat
Angola na da arzikin ma'adinaiHoto: LUCAPA DIAMOND COMPANY LIMITED/AFP

Angola kasar da ke a kan gaba wajen hako arzikin man fetir a nahiyar Afirka, da sauran ma'adinai har yanzu al'ummarta na fama da talauci da kuma rashi aikin yi, sannan ga cin hanci da karbar rashawa da suka yi wa kasar katutu. A halin yanzu, za a iya cewa, ba a san maci tuwo ba a tsakanin Adalberto Costa Júnior ɗan tsohon mai fafutukar kwato 'yanci  na UNITA wanda mahaifisa ya yi gwagwarmaya tare da tsohon jagoran UNITA Jonas Savimbi, da bayan ya dawo daga Portugal inda  ya karanci injiniyan lantarki Da kuma João Lourenço mai shekaru 68  na jam'iyyar ta MPLA , tsohon gwamnan kana tsohon ministan tsaro, kafin a shekarar 2017, José Eduardo dos Santos ya zabeshi a matsayin magajinsa.