Bude ofishin jakadanci a Kudus ya jawo rikici
May 17, 2018Talla
A ranar Litinin ce dai aka bude ofishin jakadancin na Amirka a birnin Kudus, abin da ke zuwa bayan da Shugaba Donald Trump a watan Disamba ya bayyana amincewa da birnin na Kudus a matsayin babban birnin Isra'ila, matakin da ya ce aniya ce ta Amirka tsawon shekaru, wanda sai a wannan lokaci mahukuntan na birnin Washington suka aiwatar.
Falasdinawa dai da ke fatan ganin gabashin na birnin Kudus ya zama babban birnin kasarsu sun yi tofin Allah tsine da matakin na Trump, yayin da sauran kasashe ke nuna fargabar cewa hakan na iya kunna rikici da Falasdinawa a yamma da kogin Jodan da yankin Gaz, a inda tuni sojan Isra'ila suka bindige Falasdinawa sama da 60 yayin da wasu sama da 2000 suka jikkata a kan iyakarsu da Gaza.