1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matasa za su kwato mulkin Siriya in ji Iran

December 22, 2024

Babban jagoran addini na kasar Iran Ayatollah Ali Khamenei ya yi hasashen barkewar sabon gangamin adawa da sabbin jagororin kasar Siriya bayan faduwar gwamnatin Bashar Assad.

https://p.dw.com/p/4oUL0
Hoto: Office of the Iranian Supreme Leader/AP/picture alliance

 A yayin wani taron addini da ya jagoranta a wannan Lahadi a birnin Tehran, Khamenei, ya ce matasan Siriya ba za su nade hannayensu su zura wa abin da ke faruwa a kasarsu ido ba, domin hakan shi ne zai ceto makomarsu a nan gaba. 

Faduwar gwamnatin Assad dai ta gigita kasar Iran wacce ta dauke shi a matsayin amini na kut-da-kut a Gabas ta Tsakiya. A karkashin mulkin Assad, Siriyan, ta zama wata hanya da Iran ke bi wajen isar da makamai ga kungiyar Hezbollah a Lebanon, lamarin da ya samar da fahimtar juna a tsakanin Assad da mahukuntan Iran, wadanda suka rika tallafa masa da kudade da ma makamai a yakin basasar da Siriyan ta kwashe shekaru tana cikin sa.

Tuni dai hukumomi a Tehran suka ayyana kungiyar  Hayat Tahrir al-Sham wadda ta kifar da gwamnatin Assad a matsayin ta 'yan ta'adda.