1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaSiriya

Siriya ta yi sulhu da kungiyoyi masu dauke da makamai

December 24, 2024

Yarjejeniyar da ke zama wani yunkuri na sake gina Siriya ta biyon bayan wata ganawa tsakanin shugabannin kungiyoyi da ke dauke da makamai da sabon jagoran kasar Ahmad Al-Charaa wanda ya kifar da al-Assad.

https://p.dw.com/p/4oYhm
Syrien | HTS-Anführer Muhammad Al-Dscholani
Hoto: Balkis Press/ABACA/Imago Images

Kungiyoyin da ke dauke da makamai a Siriya sun cimma yarjejeniya a wannan Talata da sabbin hukumomin kasar, wadda ta jibanci ajiye makamai domin bai wa mayakansu aiki a ma'aikatar tsaro. 

Karin bayani: Ina makomar Siriya bayan kifar da gwamnati?

Kawo yanzu wannan yarjejeniyar ba ta shafi mayakan Kurdawa masu samun goyon bayan Amurka ba, wandanda ke rike da wasu yankuna da dama a arewa maso gabashin kasar.

Sai dai kakakin sabbin hukumomin Siriyar Farhad Chami ya ce za su tattauna kai tsaye da shugabannin mayakan Kurdawan nan zuwa gaba amma ba tare da tsoma bakin wasu manyan kasashen duniya ba.

Wannan yarjejeniya da ke zama wani yunkuri na sake gina Siriya ta biyo bayan ganawar da aka yi tsakanin shugabannin kungiyoyi da ke dauke da makamai da sabon jagoran kasar ta Siriya Ahmad Al-Charaa wanda ya kifar da Shugaba al-Assad makonni biyu da suka gabata.