Jamus: Kyamar Yahudawa na karuwa a cikin al'umma
December 29, 2023'Yan sandan Jamus sun ce ana ci gaba da samun masu tsattsauran ra'ayin kyamar Yahudawa na karuwa a cikin al'umma tun bayan harin Hamas tun bayan harin da Hamas ta kaddamar kan Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba, 2023.
Rundunar 'yan sandan ta ce ta samu korafe-korafe kimanin 1,100 da ke da alaka da nuna kyama ga Yahudawa kuma ke da nasaba da al'muran da suke faruwa a Gabas ta Tsakiya, tun daga lokacin da Hamas ta kai harin har zuwa 21 ga watan nan na disamba, 2023.
Jami'an sashen bincike da kuma dakile aikata munanan laifuka ta rundunar 'yan sandan Jamus sun ce galibin wadanda aka samu da laifin sun hadar da wadanda su ka lalata kadarori ko kuma wadanda ke yada kalaman kiyayya.
A watan nuwamba 2023, ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar Jamus ta ce an samu rahotannin kyamar Yahudawa 2,874, tun daga farkon shekarar, ciki har da rahotanni 88 da ke da alaka da tarzoma.