Sudan : Juyin mulkin da ya bar baya da kura
October 29, 2021Masu zanga-zangar adawa da mukin sojin sun yi tattaki a manyan biranen kasar ta Sudan bayan kammala Salar Jumma,a. Sun cigaba da jaddada bukatarsu ta ganin an dawo da gwamnatin Abdallah Hamdok, firaministan Sudan da sojoji suka hambarar. Wasu dai har sun yanke wa sojojin wa‘adin su dawo da gwamnatin farar hula ko talakawa su tsigesu da karfin Allah, kamar yadda wannan dan kasar Sudan ke cewa."Gwamnatin farar hula muke so.In har muryar talaka ake saurare,to muna son nan da mako guda, a dawo da mulkin farar hula a Sudan,ko shi kansa Burhan ya gamu da gamonsa. Mulkin farar hula muke so ya kai Burhan."
An samu arangama a garuruwan Khartoum da Umdurman, yadda aka sanar da kashe mutum guda da jikkata wasu gwammai, lamarin da ya sanya yawan wadanda suka mutu cikin tsukin mako guda da fara boren ya kai mutane 11, amma duk da hakan ga dukkan alamu masu zanga-zangar ba su karaya ba.
Karin bayani: Abdallah Hamdok ya koma gidansa
Wani dan Sudan ya ce "Muna matukar bakin ciki da kashe mutane da sojoji ke yi don kawai suna so karfi da yaji su mulki jama,a. Muna tuna musu cewa, ko ba dade ko ba jima, duk wanda ya zubar da jinin talakawa shi ma za,a zubar da nasa jinin." Ko bayan wannan matsin lambar da sojojin na Sudan ke fuskanta daga cikin gida, daga ketare ma an sa musu kahon zuka kan su gaggauta mika mulki ga farar hula, yadda aka mayar da Sudan saniyar ware bayan da Kungiyar Tarayyar Afirka ta sanar da dakatar da kasar ta Sudan daga zama memba a cikinta har sai an mika muki ga farar hula, a yayin da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya shi ma ya yi ‘tofin Alla tsine’ da kafar ungulun da sojojin ke kokarin yi ga shirin mika mulki ga farar hula.
Karin bayani: Dambarwar rikicin juyin mulki
Irin wannan matsin lambar ta sanya sojojin suka fara lashe amansu, yadda aka ji shugaban sojin na Sudan Abdulfattah Burhan na cewa. "Za mu kammala dukkanin matakan tabbatar da adalci cikin tsukin mako guda ko kwanaki goma. Muna gayyatar Firaminista Hamdok da ya zo ya sake kafa wata sabuwar gwamnatin. Babu wanda zai masa katsalandam a zabinsa."
Tuni ofishin Abdallah Hamdok din ya sanar da cewa, shi har yanzu bai lamunta da batun tsigeshi da sojojin ke ikirarin yi ba, ballantana ace za a sake bukatarsa da ya kafa wata sabuwar gwamnatin, yana mai kira da a gaggauta sako sauran ministocinsa da ake tsare da su, don su ci gaba da aikinsu da kundin tsarin mulki da al,ummar Sudan ta dora musu.